Monday, 17 November 2025

 Military Commander in Zaria: 

"Set them on fire!"


By Usman Hafiz



My life in Tudun Wada Dankade was shattered by news from Zaria on December 12th, 2015. I was teaching at an Islamic centre. I immediately halted the lesson, telling my colleague I had to go. He lacked the money, so I sold my brand new phone to fund our journey. After sending the SIM to my wife, we left for the last major junction to Zaria.


In Zaria, soldiers had blocked all access to Hussainiyya. We navigated footpaths to Gyallesu instead. Upon arrival, we were given tasks—then the soldiers came. They opened fire as we chanted Allahu akbar. We evacuated martyrs and the wounded until morning.


At dawn, the shelling resumed. A bullet tore through my lower abdomen. I was taken to Sheikh Maina’s residence, a shelter for the wounded that became a trap. The soldiers stormed the house and massacred hundreds. Then their commander arrived.


“Is it impossible to kill them all? I beg, set them on fire!” he ordered.


Soldiers climbed the roof and poured petrol. Inside, the dead lay beside the dying. I heard the commander’s command, then the ignition. The building erupted. They shot anyone who stirred in the smoke. Eight shots were fired toward me; one found its mark. I feigned death, enduring the encroaching flames.


A burning brother phoned his family, describing our fate alive. He spoke until he was unrecognizable, dying with his face covering the phone. His family kept calling, unaware. The fire licked around me, dying down each time it neared—a miracle in the inferno. Soldiers fanned the flames with more petrol, burning most bodies to cinder.


When they stepped back, I rose painfully among the dead. I changed my blood-soaked shirt for a martyr's. I was not alone; six others survived. One, near the gate, signaled the soldiers' movements with his hand. We were too exhausted to flee.


The soldiers returned, spotted me, and argued over my fate. They dragged us out, beating us, then took us for interrogation. An officer boasted of single-handedly arresting Sheikh Zakzaky. Later, a soldier in the vehicle offered sympathy and water, a fleeting humanity. But as we reached Basawa Barrack, his tone shifted. “This place is not a hospital,” he warned. “They will torture you.”


They beat us with belts, gun butts, and boots, targeting our wounds. They threw us into an icy swimming pool, then a cell, continuing the torture. Eventually, they dumped us at a hospital.


There, I met a boy who had been with Sheikh Zakzaky. He described how they moved rooms as fire consumed the house. The Sheikh refused to surrender, and his followers refused to abandon him. Looters found them, leading the soldiers back. The soldiers noted the fearlessness of the Sheikh’s daughter before taking them away.


I contacted Malam Yahaya Bargi, who came to the hospital for us. Back in Kano, I underwent surgery for my injuries. This is what I witnessed. May Allah grant us salvation, fortitude, and the freedom of our leader.


Culled from the book "Survivors of the December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria: The Unsilenced Voices". 


Get your copy of "Survivors of the December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria: The Unsilenced Voices" @ https://selar.com/837l71

Or simply contact +2348037023343 via WhatsApp to purchase the softcopy of the book.


#Hussainiyya #ZariaMassacre #FaithUnderFire 

 #genocide

#nigeria 

#AmnestyInternational

Friday, 14 November 2025

 ALMIZAN A SHEKARA 30


Daga Haruna U. Jahun



Sannu a hankali a watan Rajab din nan na shekarar 1441, jaridar ALMIZAN cika shekaru 30 cif-cif da samuwa. Idan abin mu kwatantata da rayuwar dan’adam ne, sai a ce ALMIZAN ta fara tsallake shekarun wargi da kuriciya, ta kama hanyar shiga shekarun girma. Abin godiya ga Allah ne cewa duk da rashin takamaiman hanyoyin kudaden shiga, musamman manya-manyan tallace-tallace wadanda galibi da irin su kamfanonin jaridu suke dogara domin dorewar jarida ba kudaden farashin da masu karatu ke siyan jaridar ba, amma ALMIZAN ta shafe wadannan shekaru tana fitowa duk mako. Banda rashin kudi akwai sauran kule masu tarin yawa, musamman kasantuwarta jaridar da ba ta dasawa da gwamnatoci, wanda wannan ma kadai ya isa ya durkusar kowace irin jarida duk da irin makarantanta, a kuma kowane yanki na kasar nan balle a duniyar Hausawa da ba su dauki jarida da kima ta kwabo ba.


A kai na, ALMIZAN tana daya daga cikin jaridun da suka sa min ra’ayin karantun jarida. Bilhasali ma dai ita ce farkon jaridar da na fara siya da kudina. Na fara siyan ALMIZAN a shekarar 1993 (ko da yake tun kafin na fara siya na karanta da dama) a lokacin farashin kudinta Naira biyar ne. Har yanzu ban manta kanun labarinta ba “Danjuma da Obasanjo Sun Yi Wa Babangida Kaca-Kaca”. Ta fito ne lokacin za~en 12 ga watan Yuni na 1993 tsakanin MKO Abiola da Bashir Tofa, wanda Babangida daga baya ya soke za~en.


A dan abin da na sani a Arewa an yi kamfanonin jarida daban-daban, wanda a halin yanzu tuntuni sun fada kwandon sharar tarihi. A lokacin da aka samar da ita akwai wasu jaridun a Arewa. Ta fuskancin kwararrun ma’aikata da kudi wadannan jaridun sun yi wa ALMIZAN fintinkau. Amma kuma dalilin sadaukarwa da tsarkin niyyar ALMIZAN, sai ta zama a duk fadin Arewa babu wadda ta kai ta karade lungu da sako na nahiyar nan.


Ta fuskancin tasiri a rayuwar mutane da cusa masu ra’ayin koyon rubutu da kuma karatun boko, a kaf jaridun Hausa babu kamar ALMIZAN. Domin a shekara 30 ta zama ajin yaki da jahilci ga mutanen da yatsu ba za su dauki kidayarsu ba. A dalilin ALMIZAN wasu suka koyi karatun haruffan Hausar boko. Kuma hatta Harkar Musulunci akwai dimbim jama’a da suka fahimce ta sakamakon karanta ALMIZAN.


A fahimtar Harka kuma, ni kaina na san ALMIZAN na daya daga cikin manyan abubuwan da suka taimaka min sosai wajen fahimtarta da kuma sanin inda aka dosa. Duk da cewa lokacin da na fara Harka ba, ALMIZAN ce kadai abin da Harkar Musulunci take bugawa ba. Akwai mujallar GWAGWARMAYA da MUJAHIDAH. Akwai kuma mujallar Turanci mai suna STRUGGLE da jaridar Turanci THE POINTER. Amma yanayin da aka keto ya sanya dukka sauran sun zama tarihin da dan shekara 20 da ’yan doriya ba zai ce komai a kan su ba.


ALMIZAN ta yi tasiri sosai a fahimtata da kuma gane al’amurran yau da kullum, domin tun ina karami na taso da son karance-karance. Har yanzu babu abin da nake jin dadin sa irin karatu. Wannan ya sa nake nacin karanta jaridu da mujallun Harka kasantuwar suna kusa da ni, kuma ana buga su da harshen da nake fahimta.


Bari in dan waiwayi baya kadan. A sa’ilin da nake dan sakandire ne, fahimtata da harshen Turanci bai taka kara ya karya ba. Wannan shi ma ya sa na takaitu da karatun ALMIZAN da kuma mujallar GWAGWARMAYA. ALMIZAN tana fitowa duk mako, mujallar kuma duk wata.


Kowacce daga cikin wadannan ban da labarai da suke yi akwai wasu ~angarori da nake jin dadinsu sosai. Alal misali, a GWAGWARMAYA ina matukar jin dadin shafin “Shanshani mai kafar yawo”, wanda Danjuma Katsina yake rubutawa, kuma shi ne ma Editan mujallar.


Shi rubutu ne da yake yin sa wajen fito da halin rayuwa da al’umma ke ciki da kangin wahala da suke ciki. Bayan wannan ina son filin Tarbiyyar Iyali na Malam Husain Bauchi da filin Lafiya Uwar Jiki na Dakta Yakubu Azare da filin Tambayoyi da Amsa na Malam Ibrahim Akil. Wani lokacin ina karanta filin Tunatarwa, wanda ake kawo jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky yake yi duk mako a masallacin Jami’ar Ahmadu Bello kafin zuwan Liman.


Daga baya an fito da mujallar MUJAHIDAH, wadda Shaikh Abdulhameed Bello yake wa Edita. An yi ta ne musamman domin Sistoci, kwatankwacin MAHJUBAH, wadda ake bugawa a Jamhuriyyar Musulunci ta Iran. Abubuwan da suke cikinta ya fi shafar mata, duk da cewa ina karantata, amma dai ni ba ni da wani ~angare da ya fi daukar hankalina a cikinta. Da GWAGWARMAYA da MUJAHIDAH ina jin babu kwafin da ban karanta ba daga farkon fitowarsu, zuwa bugun wanda daga shi ba a sake wani ba.


Kamar yadda na ambata a baya, a Arewa babu al’adar karatun jarida ko mujalla. Shi Bahaushe ya fi matukar mutunta radiyo da dogara da ita a sha’anin labari fiye da jarida. Sa~anin Bayarabe da ya fi karkata da jarida da kuma talabijin. Wannan yana daga cikin dalilin da ke jawo ta~ar~arewar harkar jarida a duniyar Bahaushe. Shi ya sa duk kamfanin jaridar da aka bude bai cika daukar tsawon lokaci ba sai a neme shi a rasa. Da haka irin su mujallar RANA ta Alhaji Hassan Kwantagora, wanda Malam Ibrahim Sheme ya yi wa Edita suka kwanta dama.


Mujallar da nake karantawa bayan wadannan na Harka, sai wata wadda ake bugawa a Jamhuriyyar Musulunci ta Iran mai suna SAKON MUSULUNCI. Na karanta da daman su a wannan lokacin duk da cewa ita ma ba ta yi mini tasirin da na Harkar suke yi mini ba. Amma dai akwai mukalolin da nake jin dadin karantasu, cikin su akwai shafin Daular Usmaniyya na Farfesa Ibrahim Sulaiman da Yahudu Tuba Babu na Adamu Adamu Azare (wato Ministan Ilimi a Nijeriya a yanzu). Sai dai duk cikin wadannan da na ambata na fi jin dadin jaridar ALMIZAN. Saboda wasu abubuwan ni a shekaruna na lokacin ba su cika daukar hankalina ba.


Labaran ALMIZAN na lokacin caji ne da kuma jumudanci, wadanda na fi fahimtar su da jin dadin su. Domin har yanzu idan mun tuna wasu daga ciki mukan yi dariya. Ko kuma fakam da yawa idan ina son tuna baya, nakan bincika irin waɗannan tsofaffin ALMIZAN din in karanta irin wadannan labaran in yi ta dariya.


Abin mu yi waiwaye ne, wanda Bahaushe ke cewa adon tafiya, hakika an samu gagarumin ci gaba a jaridar ALMIZAN ta fuskacin tsari da inganci da kuma kwatanta gaskiyar aiki, wanda galibi abin da aka rasa a aikin jaridar yau. Jaridar da ta fara da shafi hudu, yau ga shi tanada shafuka 24. Jaridar da ta fara tun daga Editanta zuwa masu aika mata da rahotanni ba su da shaidar karatun aikin jarida balle kwarewa a fannin, yau ita ce take gogoriyo da kwararrun kamfanoni da masu karfi.


Jaridar da ta fara babu tallafin Hukuma ko wasu hamshakan masu kudi, babu kuma wasu manyan tallace-tallace da za a dogara da su, yau ga shi ta yi kafuwar da wadanda aka kafa su da tallafi mai karfi a kan su ga bayanta, ita ta ga bayansu. A kasar nan da wuya ka samu wata jarida da take fadakar da mutane, take dara su a kan wani tunani irin da ALMIZAN take dora su a kai.


A makon da ya gabata lokacin bikin cika shekarar ALMIZAN 30 da aka yi a garin Bauchi, mun ji abubuwa da dama daga bakin wadanda suka sha fadi-tashin tabbatuwar jaridar da kuma rawar da ta taka wajen fadakar da al’umma. Cikin abubuwan da muka ji akwai Da’irar da aka kafa ta da karatun jaridar ALMIZAN, ita suke karantawa a wurin ta’alimominsu duk mako, yau wannan Da’irar tana nan daram.


Madalla da ALMIZAN a shekaru 30 muna jinjina da jajirtatun ma’aikatanta da gwarazan dillanta da masu girma na makarantarta. A karshe sai dai na ce babu taken da ya dace da ita kamar yadda na ji an yi mata ranar wannan taro, ALMIZAN IKON ALLAH!


An ciro rubutun nan daga Littafi: ALMIZAN: TARIHI DA GWAGWARMAYARTA


Wannan littafi dai marubuta ne na ALMIZAN kusan goma sha biyu suka bayyana irin gogayyar da suka samu a tsawon wadannan sheekaru na 35, don haka kar ka bari a bar ka a baya wajen mallakar sa.


Za ka iya mallakar littafin cikin sauki ta:

https://selar.com/12j84m


Ko kuma cikin sauki ka yi text ta WhatsApp ta wannan lambar +2348037023343, don ka sayi naka kwafen, a tura ma nantake. N1000 ne kacal.

Monday, 10 November 2025

 ALMIZAN A SHEKARU 35: ABIN DA ZAN IYA TUNAWA 


Daga Danjuma Katsina



Sha’awar karance-karance ya saka ni aikin jarida. A firamare ina cikin wadanda ake sawa su karanta littafin Hausa a gaban aji. A makarantar sakandare har suna aka lakaba mani da sunan “World master story reader.”


Na shiga jami’ar Ahamadu Bello Zariya domin karatun aikin jarida a 1990. Mune ajin farko na wannan kwas din. A nan na hadu da Malam Ibrahim Musa babban Edita, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jaridar ALMIZAN.


Wata rana ya same ni, shi da marigayi Malam Umar Chiroma, ya fada mani cewa za su kafa jarida mai suna ALMIZAN, in bayar da nawa shawarwarin a matsayina na dalibin aikin jarida. Na bayar da nawa shawarwarin, har da maganar suna. Na ce wasu a Kano sun kaddamar da wani kamfani mai suna ALMIZANI. Daga baya sun dauki sunan ALMIZAN bayan tuntuba da suka yi, har da tattaunawa da Malam Ibraheem Zakzaky (H), wanda suka kara masu da hujjar cewa akwai bambanci tsakanin ALMIZANI da kuma MIZANI. Ya ce, wancan kamfani ne, wannan kuma jarida ce.


A jami’ar ABU Zariya na rike matsayin mai hulda da jama a na kungiyar dalibai ta MSS na jami’ar, har na zama Editan mujalar MSS ta lokacin, mukamin da na rike har na bar jami’ar. A lokaci guda Malam Ibrahim Musa suna ta aikinsu na buga ALMIZAN.


A 1991 aka yi zanga-zangar mujallar Fun Times a duk fadin kasar nan, wadda muka fara ta daga jami’ar ABU Zariya. Gwamnan Katsina na lokacin ya yi barazanar kashe Malam Yakubu Yahaya Katsina. Wannan ya sanya aka sake wata zanga-zangar. Wannan ya janyo aka kama ’yan uwa da yawan gaske, ciki har da ni.


Ina tsare a ofishin ’yan sanda na Sabon gari da ke Katsina na rubuta wata takarda a kan halin da muke ciki a inda ’yan uwa suke tsare. Wannan shi ne farkon rubutu na da jaridar ALMIZAN, wanda ya tayar da kura sosai.


Kyakkykawar danganta tsakani na da Alhaji Hamid Danlami da Malam Ibrahim Musa ya sanya suka yi shawarar saka ni cikin aikin tsundum a 1992, kuma aka ba ni aikin rubuta labarai, samowa, fassarawa da kuma duk wani aikin da aka dora mani. Aikina a lokacin zan rika bin duk jaridu, mujallu, da akan sanya ni in tsamo labaran da suka dace da tsarin jaridar. Zan saurari rediyo in zakulo labarai. In ana taro a Zariya zan rika hira da ’yan uwan da suka fito daga wurare ina rubuta labarai.


Ni na fara kirkiro tsarin fassara mai ’yanci. Zan karanta sharhi ko labara da Turanci, sai in fahimci sakon labarin, sai in yi rubutu a kan haka. Daga baya na yi rubutu a kan wannan; na kare matakin da na dauka na amfani da fassara mai ’yanci. Yanzu hatta jami’o’i da sauran kafafen watsa labarai sun amince da fassara mai ’yanci.


A 1993 aka kirkiro da mujjalar GWAGWARMAYA, kuma aka ba ni matsayin Editan ta. Ina tsara labaran mujallar, ina kuma sharhi, nazari da labarai a jaridar ALMIZAN. An kuma kirkiro da mujalar mata ta Mujahidah, wadda Shaikh Abdulhamid Bello ya yi wa Edita. Ita ma na rika rubutu a cikin ta.


A mujallar GWAGWARMAYA ne na yi rubutun “Zuwa ga marubutan soyayya,” wanda marubuta suka yi wa jaridar ALMIZAN caa da mujallar da martani kala-kala, wanda lokacin kullum akwatin gidan waya din mu a cike yake da wasiku.


MANYAN HIRARKKIN AL MIZAN.


Farkon ALMIZAN, duk hirarrakin ta da Malaman Harkar Musulunci ne, sai kuma wadanda aka zalunta, sai wadanda ke goyon baya ko masu tausaya ma Harkar Musulunci, babu da ’yan siyasa ko masu mulki. A 1994 a wani zama da aka yi aka yanke shawarar a fada ma duk wakilan jaridar, kowa ya yi hira da wani babban Malami a yankinsu. Wadannan hirarraki na

lokacin sun fadada jaridar zuwa zawiyoyi da makarantu da kungiya-kungiya.


Ni na yi hira da Malam Lawal Abubakar, wanda ya gaji Shaikh Mahmud Gumi bayan rasuwar sai. Na yi hira da Shaikh Dahiru Usman Bauchi a lokacin. Na gana da Shaikh Umar Sanda, masanin ilmin falaki da taurari. Na yi hira da Shaikh Ahmad Gumbi. Na je Kano na hadu da Mal. Muhammad Bakari muka yi hira da Shaikh Nasiru Kabara, har ya ba ni kyautar littafai. Na je Sakkwato na yi hira Waziri Jjunaidu.


Haka kuma Wakilan garuruwa sun yi ta turo hirarraki, wanda aka yi ta bugawa. Hirar duk ta

doru ne a kan tarihin Malaman da gwagwarmayarsu ta neman ilmi. Mun rika kauce ma duk wata magana da za ta kawo rarraba kan musulmi da kuma cece-kuce. Na yi hira da marigayi Lawal Bala Kalarawi. 


Hirarraki uku zan iya tunawa, daya mai tayar da hankali, daya mai armashi, daya mai ban mamaki. Mai tayar da hankalin ita ce, ni na yi magana ta karshe da Malam Turi kafin a kama shi a waki’ar Abacha ta 1996. Na same shi a gidansa na Kwarbai ya yi mana magana ta karfafa gwiwa da kuma dakewa da hadin kai a komai zai faru a gaba. Kwana daya aka ce mani an kama shi. 


Ta biyu mai armashi, ita ce wadda muka yi hira da Malam Zakzaky (H), ni da Shahid Ibrahim Usman, mu uku, watanni bayan fitowar su daga gidan yari daga kamawar Abacha. Hira ta uku mai ban mamaki, ita ce hirar da na yi da Guru Maharaji na Ibadan. 


Jaridar ALMIZAN ta yi manyan hirarraki. Daga cikin su akwai da tsohon Shugaban kasa

Ibrahim Babangida, da tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa. Haka kuma ta yi hira da tsaffin manyan ’yan siyasa irin su Malam Tanko Yakasai da Lawal Dambazau da tsaffin gwamnoni da tsaffin Sarakuna. Misali Sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Shehu Idris da Sarkin Katsina marigayi Kabir Usman Nagogo. Manyan dattawa masu kishin kasa, wadanda suka sadaukar irin su M.D. Yusufu da manyan sojoji irin su Tukur Buratai, duk an yi hira da su a ALMIZAN.


MANYAN LABARAI


Jaridar ta buga manyan labarai da suka yi tasiri sosai a kasar nan, ba ma wani yanki na kasar nan ba. Wadanda suka shafe ni kai tsaye daga cikin su akwai: ZOBE MAI AMAN KUDI NA WANENE?


Wani labari ne da na rubuta a kan wani zobe mai aman kudi da aka tsinta a wani masallaci a jihar Katsina. Labari ne da aka kawo mani shi ta amintacciyar hanya. Na kara da nawa binciken na saki labarin. Ya girgiza kasar nan, an yi ta juya labarin zuwa kafa-kafa, ana canza masa salo.


Babban bakin cikina a labarin shi ne yadda aka rika daukar wani matashi wanda a lokacin yana tashen kudi, gwamnatin soja ta lokacin tana yi da shi, amma aka rika tambayar ya aka yi ya samu kudi? A labarin na ba da misalai da zai tabbtar da ba shi bane, amma makiyansa suka yi ta yada cewa shi ne.


A lokacin an yi, an yi da ni in fadi wane ne? Na ki fada. Mutum biyar kadai na fada mawa sunansa. Daga cikin su akwai marigayi MD Yusufu, wanda ya tabbatar mana da bincike ya tabbatar ba sharri nake yi ba. Mutumin da labarin ya shafa, na taba gabatar masa da kaina a wani taro a Kaduna. Sai ya kalle ni ya ce, duk bawan da ya rufa wa bawan Allah asiri, Allah zai rufa masa nasa. Nan na ji kwalla ta cika mani idanu. Mutumin, yanzu ya dade da rasuwa, kuma ya rasu da kyakkyawar shaida, duk Katsina cewa ake mutumin kirki ne.


Labari na biyu na hoton Annabi Musa (AS) da wata mujalla ta zana aka buga. Na samu mujallar ta hanyar Abdullahi Lowcost. Na rubuta labarin, na aika tare da mujallar satin da aka buga shi. Kasar nan ta dauka jaridar ALMIZAN ta buga hoton Annabin Allah.


Labari na uku shi ne na yadda ’yan JTI suka saro kan kafirin nan Gidion Akaluka a birnin Kano. Na isa Kano da yamma, na kwana. Da safe na fara binciken ya aka yi? Na gana har da Shugaban JTI na Kano a lokacin, Ahmad Shu'aibu. Na samu tabbacin me ya faru, ya aka yi lamarin?


Na dawo Zariya, na ba da labari, na kuma rubuta me na gano; na bayar aka buga. Fitar jaridar ta girgiza har da ’yan JTI da suka dauka in an tashi labarin, ba za a yi masu adalci ba. Sai ga shi labarinmu ya fi wanda suka rubuta a jaridar su adalci.


Labari na hudu na rikicin gwamnan Kano, Abdullahi Wase da gidan Kadiriyya. Gwamnatin Kano ta yi yunkurin hana taron maukibi, Shaikh Nasiru Kabara ya ce, ba su isa ba. Aka tura ni dauko rahoton. Na yi hira da Malam Nasiru Kabara a tsaye a bakin masallacin gidansa, inda ya shelanta cewa ba za su sake yarda ba a hana su taron da Allah ya halasta masu. Jaridar ta fito da hoton Malam Nasiru Kabara bisa doki da takobi a hannunsa da taken ba za mu sake yarda ba.


Labari na biyar na kisan kiyashin ’yan Tatsine a Funtuwa. A gabana aka rika kona su da rai. Mun dauki hotuna a lokacin masu tayar da hankali. Duk kasar nan, da hutunan da jaridar ALMIZAN ta buga aka rika amfani da shi. Rikici ne da ya fara daga gardama a kasuwa, ya koma kasha-kashe na duk wadanda aka ce wai ’yan Tatsine ne. Wannan gani-da-idon ya yi mani tasiri ga duk rubutuna da ayyukana na cewa, kar mu yi katanga ko shamaki da mutane. Wannan shi ne mataki mafi hatsari. Na yi wani sharhi a kan haka mai taken rikicin al’ummar

gari da ’yan Tatsine, sai kuma wa? A lokacin na ga ana danna yaro cikin wuta, yana ci, yana kokarin fita, ya tsira, ana mayar da shi. Na ga rijiyar da aka cike da mutane a ciki, don kar su fito.


Labarin zargin kwartanci da aka yi ma wani dan uwa a Sakkwato ya saka ni tsaka mai wuya, kuma daga karshe ya ba ni ruwa. Wani labarin da wata mata ta yi ma Malam Yakubu Yahya takakkiya shi ne mai taken “Saboda matan banza, ’ya’ya sun casa ubansu.” Labari ne da yarinyar da abin ya shafa, ta same ni har gida ta fada mani.


Mun yi labarai manya a rikice-rikice daban-daban lokacin shari’ar su Zamani Lekwot. Na yi shigar mata na shiga kotun. Na taba shigar mata na shiga barikin soja na Zariya. Na yi shigar kiristoci na sha shiga coci.


SHARHI DA NAZARI


Tun alakata da ALMIZAN, daga abin da na rika yi shi ne sharhi da kuma nazari wadanda za su zama hannunka mai sanda da turken mil. Na rika nazari da alakanta abin da na yi sharhi a kan shi, sannan in danganta shi da harkar Musulunci, wadda ita ce mafita. Mafi yawan lokuta, marigayi Alhaji Danlami ke dora ni hanyar me zan yi nazari, wani lokaci Edita. Wani lokaci kuma masu karatu, wani lokaci ni ke zabar ma kaina abin da zan yi rubutu a kai.


A shekaru 30 na farko na ALMIZAN ba a taba jera fitowa uku ba rubutuna ba. Na yi hannunka mai sanda a rubutuna, wanda sai daga baya aka gane me nake nufi, wasu na rubuta su shekaru goma, ashirin, ashirin da biyar, amma sakon kamar yanzu aka fade shi. Lokacin da za a mayar da fitowar jaridar sati-sati, na fito da filaye biyu da nake rubutu karkashin su. “Hantsi Leka Gidan Kowa” da kuma “Rubutu da Marubuta,” da aka fara su a 1997. Duka shafukan sun zama abokan hira ga makaranta.


DAUKO RAHOTON SHARI’AR MALAM ZAKZAKY (H) ZAMANIN

ABACHA


Lokacin shari’ar su MALAM ZAKZAKY (H) a zamanin Abacha (1997), ni na rika kawo rahoton me ke faruwa a kotun? ’Yan’uwa, an yi ta mamakin ya ake samun labarin abin da ke faruwa a kotun? Domin lokacin ana sanya mugun tsaro, kuma kusan kullum aka fita shari’ar, sai an yi zanga-zangar da za a samu shahidi. A lokacin mu hudu muka rika wannan aikin. Shaheed Ibrahim Usman yana shiga kotun da katinsa na aikin jarida na New Nigeria. Kafin shi akwai Ibrahim Dahiru, wani ma’aikaci a kamfanin Today newspapers. Shi ne kan shiga ya ba ni labari. Sai kuma wani mai suna Inuwa Bwala, yana aiki da jaridar Punch a lokacin. Sai

wata Mary Agusten da ke aiki da mujallar The news.


Haduwata da Shahid Ibrahim Usman, ofishin Malam Ibrahim Sheme na New Nigeria na fada masa abin da ke kawo ni Kaduna da yadda nake aikina. Sai muka sake tsara lalen aikin. Mun ci gaba da mu’amala har lokacin da ya bar duniya. 


LITTAFAN DA NA BUGA KARKASHIN ALMIZAN


Na rubuta littafai karkashin ALMIZAN kamar haka:

Tarihin Shaikh Usman Dan Fodiyo Don Kananan yara a 1994

Yunkurin Murkushe ’yan uwa: Zalunci ko adalci? a 1997

Malam Zakzaky: Wakilin Manzo (S) a Doron Kasa a 1998

Mai Yadda Ya So (labara na hikaya) a 1998.

Bosniya: Ta’addancin da ake wa Musulmi a 2000.

Na kuma taimaka an rubuta wasu masu yawan gaske.


TALLA A JARIDAR ALMIZAN


Ni na fara kawo tallar gwamnati a jarida, bayan mun samu amincewar Malam Zakzaky (H) na irin tallar da za mu iya bugawa. Tallar farko daga kwamitin musabakar Alkur’ani ta kasa da aka yi a Katsina ne a 1993, lokacin Justice Musa Danladi Abubakar shi ne Sakataren shirya taron. Sai Karamar hukumar Katsina, lokacin Alhaji Hamisu Gambo yana shugaban Karamar hukuma. Sai daga Ma’aikatar gona karkashin hukumar IFAD. Allah ya ji kan marigayi Shehu Bakori, ya nuna mana kauna.


Sai Alhaji Salisu Yusuf Majigiri, lokacin yana Shugaban Karamar hukumar Mashi. Ga Alhaji Bello Musa Dankano, lokacinn yana Sakataren gwamnatin Katsina. Haka nan Alhaji Umaru Musa ’Yar’adua, Gwamnan Katsina. Da Barrister Ibrahim Shema CON, Gwamnan Katsina na biyu a farar hula. Sai Hon. Aminu Bello Masari CFR, Gwamnan Katsina na uku a farar hula. Da Malam Dikko Umar Radda, Gwamnan Katsina na yanzu 2023.. 


A bangaren attajirai akwai irin su Alhaji Dahiru Barau Mangal da Alhaji Abdul Aziz Maigoro. Ban iya kawo duk sunayen wadanda na yi mu’amala da su ta samar wa ALMIZAN kudi, sai dai a ce Allah ya saka da alheri. Na ji daga bakin Alhaji Danlami cewa Alhaji MD Yusufu, shi ma ya sha taimakon jaridar da taimakon kudi kai tsaye daga aljihunsa.


ALHAJI HAMIDU DANLAMI DA MALAM IBRAHIM MUSA


Marigayi Alhaji Hamidu Danlami, Manajin-Daraktan kamfanin I.M Publications mai buga jaridar ALMIZAN da Malam Ibrahim Musa, babban Editan ALMIZAN, sune jigo, turaku, ginshikai, kuma rumfa na kafuwar jaridar ALMIZAN. Duk wata nasara da aka samu na wadannan shekaru sune. Sun yi hakuri da mu a lokacin da muna gabar yarinta da samartaka. Sun yi hakuri da rashin wayo da gaulanci da wauta da muka rika nunawa. Sun kasance tare da mu a duk lokacin bukata, ba su taba rabuwa da mu ba a lokacin da muke neman shawararsu ko taimakonsu. Allah ya saka masu da mafificin alheri.


An ciro rubutun nan daga Littafi: ALMIZAN: TARIHI DA GWAGWARMAYARTA

Wannan littafi dai marubuta ne na ALMIZAN kusan goma sha biyu suka bayyana irin gogayyar da suka samu a tsawon wadannan sheekaru na 35, don haka kar ka bari a bar ka a baya wajen mallakar sa.


Za ka iya mallakar littafin cikin sauki ta:

https://selar.com/12j84m


Ko kuma cikin sauki ka yi text ta WhatsApp ta wannan lambar +2348037023343, don ka sayi naka kwafen, a tura ma nantake. N1000 ne kacal.


 ALMIZAN DA TALLAR TA A LOKACIN WAKI’O’I 


Daga Hasan Baffa



Jaridar ALMIZAN ta kasance daya daga cikin fitattun jaridun Hausa a Nijeriya, musamman wajen isar da sakonnin Harkar Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Tun bayan kafuwar ta a shekarar 1991, ta zama muhimmiyar kafa don yada ilimi da bayanai kan addini, zamantakewa, siyasa, wasanni, sana’a, nishadi, da labarai. 


Duk da irin nasarorin da ta samu, jaridar ta sha fuskantar manyan kalubale, musamman daga hukumomin da ke kokarin dakile ayyukanta. ALMIZAN a lokacin waki’o’i da kuma tallar ta ta bambanta da sauran jaridu domin in ana waki’a yin aikin yana kara wuya, haka ma yanayin tallar ta, yayin da kuma masu bukata ke kara yawa domin a nan ne kawai ake samun sahihin labarai da matsaya ta Harkar Musulunci. Domin duk wata sanarwa ko labari da zai fito ta kafar sadarwa na zamani (Socila Media) ba abin amincewa da dogaro ba ne


WAKI’AR ABACHA –12 GA SATUMBA, 1996


A wannan lokaci, jaridar ALMIZAN ta tsinci kanta cikin tsananin matsin lamba. Bayan wani farmaki da jami’an tsaro suka kai gidan Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), an kuma kai samame gidan Shugaban Hukumar Gudanarwar jaridar; Alhaji Hamid Danlami, tare da kama shi, mataimakinsa; Malam Abubakar Abdullahi, da jami’in sashin buga jaridar; Malam Muhammad Shitu Zariya.


An kwace kayan aiki masu yawa, ciki har da kwamfutoci da kwafen jaridar da aka shirya za ta fito a wannan makon. Wannan farmaki ya sa jaridar ta zama tamkar abar tsoro ga hukumomi, inda hakan ya janyo cikas ga bugawa da rarraba jaridar, musamman a garuruwan Katsina, Kaduna, Sakkwato, Funtuwa, da kuma Zariya.


A irin waɗannan garuruwan, an sayar da jaridar ne tamkar kayan fasa kwauri ko kayan maye, inda mai saye da mai sayarwa ne kawai suka san juna. Kasantuwar mafi yawan waki’o’in sun bambanta daga jiha zuwa jiha; wasu gwamnonin sun dauki matsayar fada da Harkar, yayin da wasu suka kau da kai, domin ba za su auka wa jama’arsu ba saboda dalilai na siyasa, biyan bukatun kasashen waje, ko bambancin ra’ayi.


Masu sayarwa da rarraba jaridar sun gamu da matsaloli iri-iri, ciki har da tsarewa, duka, har ma da tilasta wa wasu yin hijira. Duk da haka, masu sayarwa sun nuna jarunta da kwazo wajen ganin jaridar ta isa ga masu karatu. Duk da mawuyacin hali, masu sayen suka nuna tsantsar soyayya da kauna ta hanyar bibiyar hanyoyin da za su samu jaridar ba tare da tsoro ko fargabar abin da zai biyo baya ba.


WAKI’AR DSS – LABARIN MATASAN YOBE


A wani lokaci, Hukumar DSS ta kama wasu ma’aikatan jaridar saboda wani labari da suka wallafa kan kama ko batan wasu matasa 71 a Potiskum na jihar Yobe. A farko, an ɗauka cewa kamun yana nasaba da wannan labari ne. Sai dai daga baya aka fahimci cewa kuskure aka yi wajen kamun. Duk da haka, lamarin ya yi matukar shafar aikin jaridar, musamman wajen samun bayanai cikin sauki.


Sai dai kungiyoyin ’yan jarida ta kasa da na Afrika sun shiga tsakani, har aka samu sakin wadannan ma’aikata ba tare da sun dauki lokaci mai tsawo a tsare ba.


WAKI’AR BUHARI – 12 GA DISAMBA, 2015


Wannan waki’a ita ce mafi tsanani da girma a tarihin Harkar Musulunci. Duk da kasancewar a lokacin an samu ci gaban fasahar sadarwa irin ta Intanet da wayoyin hannu (GSM), matsin tattalin arziki da durkushewar darajar Naira sun yi matukar shafar aikin ALMIZAN, inda hakan ya sa jaridar ta rinka samun matsalolin fitowa akai-akai.


Waki’ar Buhari ta bambanta da ta Abacha sosai. A lokacin Abacha, daidaiku da tarukan Harkar Musulunci ne ake farmaka, yayin a lokacin Buhari, farmakin ya shafi duk wani motsi da halartar tarukan Harkar ne kawai ake aukawa.


Har ila yau, kisan kiyashin Zariya ya rutsa da fiye da mutum dubu, inda suka rasa rayukansu. Duk da gwamnati ta tabbatar da kashe mutum 347 ne, kamar yadda Sakataren Gwamnatin jihar Kaduna, Abbas ya tabbatar a gaban kwamitin bincike da bin diddigin abin da ya faru (JCI).


Wannan kisan kiyashin da gwamnati ta yi, ya rutsa da wakilai da dillalan jaridar da dama. Wannan lamari ya kara jefa ta cikin wani yanayi da har yanzu ba a iya cike gurbin wasu ba.


KALUBALEN AIKI DA KARFIN GWIWA


Duk da kalubalen karancin kayan aiki, tsangwama daga hukumomi, da karancin kudaden da uwa-uba wahalar hada kudaden ciniki a lokacin waki’a, kasantuwar abubuwan da kan-je-ya-dawo na yau da kullum, jaridar ALMIZAN ta taka rawar gani wajen isar da sakonnin Harkar Musulunci. Ta tsaya tsayin daka kan manufofinta, ba tare da karkata ba, duk da irin sukar da ta sha fuskanta daga ciki da wajen Harkar. Ta tsaya kyam a kan manufofi da ka’idoji na aikin jaridar (Editorial Policy).


KAMMALAWA


A yau, jaridar ALMIZAN ta kasance wata sahihiyar kafa ta samun bayanai ga mabiyan Harkar Musulunci da al’umma gaba daya. Duk da matsalolin da ta fuskanta a tsawon shekaru 35, jaridar ta zama alamar jajircewa da gwagwarmaya wajen isar da sako mai ma’ana ga al’umma. Kuma masu tallan ta a shirye suke su bi duk hanyoyi na zamani da kuma fuskatar duk wata waki’a wajen sauke wannan nauyin da ke kansu.


An ciro rubutun nan daga Littafi: ALMIZAN: TARIHI DA GWAGWARMAYARTA


Wannan littafi dai marubuta ne na ALMIZAN kusan goma sha biyu suka bayyana irin gogayyar da suka samu a tsawon wadannan sheekaru na 35, don haka kar ka bari a bar ka a baya wajen mallakar sa.


Za ka iya mallakar littafin cikin sauki ta:

https://selar.com/12j84m

Ko kuma cikin sauki ka yi text ta WhatsApp ta wannan lambar +2348037023343, don ka sayi naka kwafen, a tura ma nantake. N1000 ne kacal.

 Hellfire in Zaria: I Saw the Three Trucks Loaded with the Dead


By Musa Muhammad Waki’a



The news from Zaria found us on the road to Nasarawa that Saturday, a stark interruption that turned our car around. We arrived in Gyallesu under the cover of darkness, only to find the streets choked by soldiers. Every path was sealed. Our only way in was through the clinging cold of a swamp, our movements furtive as we slipped past the final military checkpoint closing in on the Sheikh’s gate.


Dawn broke on Sunday not with light, but with the sound of stones clattering against armored steel. Our pathetic arsenal was met with the deafening crack of shelling. They advanced relentlessly, a wall of fire and metal, and when their push ended, the air was thick with silence. So many were gone. We, the last handful, retreated into the house, listening to the soldiers’ boots crunching outside in the gravel.


Our final, desperate strategy was a grim procession: we would go out one by one. Each man who stepped through the doorway was met with a volley of shots, his body crumpling before he could take three steps. When my turn came, I filled my lungs with the name of God. “Allahu Akbar.” I chanted it like a mantra, walking into the storm. The first bullet hit, a searing punch, but my legs kept moving. It was the second, shattering my thigh, that finally sent me to the ground. Then, the world dissolved into muzzle flashes and the dull thud of boots against my body. I felt a sting on my scalp, and then the warm, relentless flow of blood. The beating only stopped when I no longer flinched.


I lay there, playing dead, as the soldiers moved with grisly efficiency. They piled the lifeless and the nearly-lifeless together. Then they called in the thugs, who descended like vultures to pick pockets and strip watches from the fallen. It was the chill of the morning dew seeping into my wounds that shocked me back to consciousness.


Through a haze of pain, I saw them bring three massive military trucks. They loaded the bodies, stacking them until the vehicles groaned under the weight. A soldier’s voice, distorted by a loudspeaker, demanded the Sheikh. When no answer came, the air sharpened with the smell of petrol. A match was struck, and the house erupted.


The heat was a physical force. Inside, the screams of women and children twisted together with the roar of the flames. A soldier stood near me, unmoved, and said, “You will die to meet another round of tortures in hell.” A bulldozer growled to life, its metal jaw tearing into the building’s side, allowing the soldiers to pour bullets into the exposed rooms. They finally dragged the Sheikh out, bleeding from multiple wounds, and mocked him. “This is the beginning of your end.” I saw them pull his wife away. I heard a soldier declare the Sheikh dead. Then, they cut the power, scaled the walls, and rained explosives down from above, ensuring nothing inside remained.


For those of us who had survived the massacre, a new ordeal began. We were taken to the barracks, where torture was a rigorous, insulting addition to our injuries. They bound us tightly and threw us into an underground dungeon, a tomb for the living. Later, we were transferred to a larger room, where over a hundred broken brothers and sisters huddled together. Our final destination was a cold floor at the ABU Teaching Hospital in Shika, where the soldiers dumped us, their final act of disposal for the broken and the scarred.


Culled from the book "Survivors of the December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria: The Unsilenced Voices". 


Get your copy of "Survivors of the December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria: The Unsilenced Voices" @ https://selar.com/837l71

Or simply contact +2348037023343 via WhatsApp to purchase the softcopy of the book.


#Hussainiyya #ZariaMassacre #FaithUnderFire #SurvivorStory #genocide

 Shot at Seventeen: My Harrowing Experience with Soldiers in Zaria


By Fatima Halilu



I was 17 years old and in my final year of secondary school when I was shot in Gyallesu, Zaria, on December 12, 2015. I was hit twice—once in the foot and once in the shoulder. They also aimed at my head. The scars remain. Soldiers shot me and took me to their barracks in Basawa. 


That day, my mother called to check on me. I told her I was home, but she urgently asked me to go to the Sheikh’s house because it was under attack and soldiers were killing people. I went with my friend Momi. As soon as we arrived, we saw soldiers shooting at everyone. We ran to a house where our brothers cooked and started preparing food. As we ate, gunfire grew closer. One brother warned the soldiers had almost reached the Sheikh’s house. Everyone rushed to the door, including us.


Outside, we found our brothers taking cover on the ground. We encouraged them, hoping soldiers might spare women if we confronted them. But as soon as we stepped out, soldiers shot two sisters dead—one in the chest, another in the head. We carried them back inside. Seconds after stepping out, I was shot in the shoulder and fell. I helped a wounded brother until some sisters arrived. Then a bullet shattered my leg. 


As we tried to return inside, soldiers caught us and ordered us to surrender. They arrested us, searched the sisters, tore off hijabs, tied our hands behind our backs, and threw us in their vehicle heading to Basawa barracks. We were locked in a dark room with men and women crammed together. One brother suggested sisters stay behind the brothers for cover since many had torn clothes and no hijabs. Some brothers gave their clothes to the sisters to protect them from the cold.


The soldiers ignored our injuries and gave no medical help. Food arrived only in the morning—biscuits and lemon drink, then rice and water. Later, the soldiers brought out the women, moved us to a different room, gave us water, and recorded our names. They then took us to a police station in Kaduna. 


The police released us days later, apologizing for what happened. They did not abuse us, though they were firm. I overheard a soldier say, “It’s a shame we were sent to kill women and children. Most are under 20. This wasn’t a war we should fight. We were lied to, told we’d fight heavily armed enemies.” I recognize him because he and another soldier often visited us, bringing supplies and showing sympathy.

Culled from the book "Survivors of the December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria: The Unsilenced Voices". 

Get your copy of "Survivors of the December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria: The Unsilenced Voices" @ https://selar.com/837l71

Simply contact +2348037023343 via WhatsApp to purchase the softcopy of the book.


Saturday, 8 November 2025

 Bullet in the Shoulder: My Desperate Escape from the Hussainiyya Killing Fields


By Aliyu Muhammad Gummi


​I am a 36-year-old NCE holder and trader in Zaria. I witnessed the massacre that unfolded on December 12, 2015.


​Around noon, I learned of the growing standoff at Hussainiyya in the Tudun Wada area, where soldiers had been deployed. Advised to rush there, I rode my motorcycle and immediately encountered battle-geared soldiers near PZ. I saw volunteers occupying the Hussainiyya gates while brothers attempted to speak with a senior army officer. I was informed that soldiers had already opened fire and killed people prior to my arrival.


​I watched as determined brothers lay on the road to prevent military vehicles from reaching the compound. At this point, I noticed soldiers were actively videotaping the scene. I immediately sensed a conspiracy—a deceptive military tactic to create a false record to justify their actions. My premonition was instantly confirmed when the camera crew left, and nonstop, indiscriminate gunfire erupted.


​We swiftly evacuated Sheikh Zakzaky’s sons, Sayyid Ali and Sayyid Humaid, to prevent a repeat of the Quds Day tragedy. Remaining on the road, I was forced to lie flat as high-caliber weapons fired for over thirty minutes. It became clear the military invasion was premeditated, as soldiers quickly moved into the polo pitch and toward Hussainiyya, disproving any claim that the attack was merely a response to a blocked convoy.


​From behind a makeshift pavilion, I watched in horror as soldiers executed the brothers and sisters who had lain on the road. I witnessed the murder of Fatima, a young sister and daughter of Alhaji Uncle, who was shot down. Her father rushed to save her but was also shot dead. The soldiers ensured each victim was followed up with a final bullet to the head or chest. The atrocities continued as army vehicles brutally ran over the bodies scattered across the road.


​When soldiers finally spotted me, I ran into the railway station under fire. I stumbled, and a bullet struck my shoulder. Though bleeding severely, I managed to disappear into the station, where hidden brothers aided my escape on a commercial bike and a tricycle, detouring through the city.


​Despite my injury, I pleaded to be taken to the Sheikh’s Gyallesu residence, fearing for his safety, but volunteers insisted on medical care. I was taken to the few remaining medics, received first aid, and was sheltered overnight. The next morning, news arrived that soldiers were searching houses for survivors. Advised to flee Zaria immediately, I traveled to Gusau for surgery.


​On the journey, I saw military checkpoints, tanks, and soldiers shooting our brothers at a checkpoint in Randar Kano. I safely reached Gusau, where a senior movement member ensured I received the necessary surgery. May Allah protect our leader and grant our martyrs peace. Ameen.


Culled from the book "Survivors of the December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria: The Unsilenced Voices".