ALMIZAN A SHEKARA 30
Daga Haruna U. Jahun
Sannu a hankali a watan Rajab din nan na shekarar 1441, jaridar ALMIZAN cika shekaru 30 cif-cif da samuwa. Idan abin mu kwatantata da rayuwar dan’adam ne, sai a ce ALMIZAN ta fara tsallake shekarun wargi da kuriciya, ta kama hanyar shiga shekarun girma. Abin godiya ga Allah ne cewa duk da rashin takamaiman hanyoyin kudaden shiga, musamman manya-manyan tallace-tallace wadanda galibi da irin su kamfanonin jaridu suke dogara domin dorewar jarida ba kudaden farashin da masu karatu ke siyan jaridar ba, amma ALMIZAN ta shafe wadannan shekaru tana fitowa duk mako. Banda rashin kudi akwai sauran kule masu tarin yawa, musamman kasantuwarta jaridar da ba ta dasawa da gwamnatoci, wanda wannan ma kadai ya isa ya durkusar kowace irin jarida duk da irin makarantanta, a kuma kowane yanki na kasar nan balle a duniyar Hausawa da ba su dauki jarida da kima ta kwabo ba.
A kai na, ALMIZAN tana daya daga cikin jaridun da suka sa min ra’ayin karantun jarida. Bilhasali ma dai ita ce farkon jaridar da na fara siya da kudina. Na fara siyan ALMIZAN a shekarar 1993 (ko da yake tun kafin na fara siya na karanta da dama) a lokacin farashin kudinta Naira biyar ne. Har yanzu ban manta kanun labarinta ba “Danjuma da Obasanjo Sun Yi Wa Babangida Kaca-Kaca”. Ta fito ne lokacin za~en 12 ga watan Yuni na 1993 tsakanin MKO Abiola da Bashir Tofa, wanda Babangida daga baya ya soke za~en.
A dan abin da na sani a Arewa an yi kamfanonin jarida daban-daban, wanda a halin yanzu tuntuni sun fada kwandon sharar tarihi. A lokacin da aka samar da ita akwai wasu jaridun a Arewa. Ta fuskancin kwararrun ma’aikata da kudi wadannan jaridun sun yi wa ALMIZAN fintinkau. Amma kuma dalilin sadaukarwa da tsarkin niyyar ALMIZAN, sai ta zama a duk fadin Arewa babu wadda ta kai ta karade lungu da sako na nahiyar nan.
Ta fuskancin tasiri a rayuwar mutane da cusa masu ra’ayin koyon rubutu da kuma karatun boko, a kaf jaridun Hausa babu kamar ALMIZAN. Domin a shekara 30 ta zama ajin yaki da jahilci ga mutanen da yatsu ba za su dauki kidayarsu ba. A dalilin ALMIZAN wasu suka koyi karatun haruffan Hausar boko. Kuma hatta Harkar Musulunci akwai dimbim jama’a da suka fahimce ta sakamakon karanta ALMIZAN.
A fahimtar Harka kuma, ni kaina na san ALMIZAN na daya daga cikin manyan abubuwan da suka taimaka min sosai wajen fahimtarta da kuma sanin inda aka dosa. Duk da cewa lokacin da na fara Harka ba, ALMIZAN ce kadai abin da Harkar Musulunci take bugawa ba. Akwai mujallar GWAGWARMAYA da MUJAHIDAH. Akwai kuma mujallar Turanci mai suna STRUGGLE da jaridar Turanci THE POINTER. Amma yanayin da aka keto ya sanya dukka sauran sun zama tarihin da dan shekara 20 da ’yan doriya ba zai ce komai a kan su ba.
ALMIZAN ta yi tasiri sosai a fahimtata da kuma gane al’amurran yau da kullum, domin tun ina karami na taso da son karance-karance. Har yanzu babu abin da nake jin dadin sa irin karatu. Wannan ya sa nake nacin karanta jaridu da mujallun Harka kasantuwar suna kusa da ni, kuma ana buga su da harshen da nake fahimta.
Bari in dan waiwayi baya kadan. A sa’ilin da nake dan sakandire ne, fahimtata da harshen Turanci bai taka kara ya karya ba. Wannan shi ma ya sa na takaitu da karatun ALMIZAN da kuma mujallar GWAGWARMAYA. ALMIZAN tana fitowa duk mako, mujallar kuma duk wata.
Kowacce daga cikin wadannan ban da labarai da suke yi akwai wasu ~angarori da nake jin dadinsu sosai. Alal misali, a GWAGWARMAYA ina matukar jin dadin shafin “Shanshani mai kafar yawo”, wanda Danjuma Katsina yake rubutawa, kuma shi ne ma Editan mujallar.
Shi rubutu ne da yake yin sa wajen fito da halin rayuwa da al’umma ke ciki da kangin wahala da suke ciki. Bayan wannan ina son filin Tarbiyyar Iyali na Malam Husain Bauchi da filin Lafiya Uwar Jiki na Dakta Yakubu Azare da filin Tambayoyi da Amsa na Malam Ibrahim Akil. Wani lokacin ina karanta filin Tunatarwa, wanda ake kawo jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky yake yi duk mako a masallacin Jami’ar Ahmadu Bello kafin zuwan Liman.
Daga baya an fito da mujallar MUJAHIDAH, wadda Shaikh Abdulhameed Bello yake wa Edita. An yi ta ne musamman domin Sistoci, kwatankwacin MAHJUBAH, wadda ake bugawa a Jamhuriyyar Musulunci ta Iran. Abubuwan da suke cikinta ya fi shafar mata, duk da cewa ina karantata, amma dai ni ba ni da wani ~angare da ya fi daukar hankalina a cikinta. Da GWAGWARMAYA da MUJAHIDAH ina jin babu kwafin da ban karanta ba daga farkon fitowarsu, zuwa bugun wanda daga shi ba a sake wani ba.
Kamar yadda na ambata a baya, a Arewa babu al’adar karatun jarida ko mujalla. Shi Bahaushe ya fi matukar mutunta radiyo da dogara da ita a sha’anin labari fiye da jarida. Sa~anin Bayarabe da ya fi karkata da jarida da kuma talabijin. Wannan yana daga cikin dalilin da ke jawo ta~ar~arewar harkar jarida a duniyar Bahaushe. Shi ya sa duk kamfanin jaridar da aka bude bai cika daukar tsawon lokaci ba sai a neme shi a rasa. Da haka irin su mujallar RANA ta Alhaji Hassan Kwantagora, wanda Malam Ibrahim Sheme ya yi wa Edita suka kwanta dama.
Mujallar da nake karantawa bayan wadannan na Harka, sai wata wadda ake bugawa a Jamhuriyyar Musulunci ta Iran mai suna SAKON MUSULUNCI. Na karanta da daman su a wannan lokacin duk da cewa ita ma ba ta yi mini tasirin da na Harkar suke yi mini ba. Amma dai akwai mukalolin da nake jin dadin karantasu, cikin su akwai shafin Daular Usmaniyya na Farfesa Ibrahim Sulaiman da Yahudu Tuba Babu na Adamu Adamu Azare (wato Ministan Ilimi a Nijeriya a yanzu). Sai dai duk cikin wadannan da na ambata na fi jin dadin jaridar ALMIZAN. Saboda wasu abubuwan ni a shekaruna na lokacin ba su cika daukar hankalina ba.
Labaran ALMIZAN na lokacin caji ne da kuma jumudanci, wadanda na fi fahimtar su da jin dadin su. Domin har yanzu idan mun tuna wasu daga ciki mukan yi dariya. Ko kuma fakam da yawa idan ina son tuna baya, nakan bincika irin waɗannan tsofaffin ALMIZAN din in karanta irin wadannan labaran in yi ta dariya.
Abin mu yi waiwaye ne, wanda Bahaushe ke cewa adon tafiya, hakika an samu gagarumin ci gaba a jaridar ALMIZAN ta fuskacin tsari da inganci da kuma kwatanta gaskiyar aiki, wanda galibi abin da aka rasa a aikin jaridar yau. Jaridar da ta fara da shafi hudu, yau ga shi tanada shafuka 24. Jaridar da ta fara tun daga Editanta zuwa masu aika mata da rahotanni ba su da shaidar karatun aikin jarida balle kwarewa a fannin, yau ita ce take gogoriyo da kwararrun kamfanoni da masu karfi.
Jaridar da ta fara babu tallafin Hukuma ko wasu hamshakan masu kudi, babu kuma wasu manyan tallace-tallace da za a dogara da su, yau ga shi ta yi kafuwar da wadanda aka kafa su da tallafi mai karfi a kan su ga bayanta, ita ta ga bayansu. A kasar nan da wuya ka samu wata jarida da take fadakar da mutane, take dara su a kan wani tunani irin da ALMIZAN take dora su a kai.
A makon da ya gabata lokacin bikin cika shekarar ALMIZAN 30 da aka yi a garin Bauchi, mun ji abubuwa da dama daga bakin wadanda suka sha fadi-tashin tabbatuwar jaridar da kuma rawar da ta taka wajen fadakar da al’umma. Cikin abubuwan da muka ji akwai Da’irar da aka kafa ta da karatun jaridar ALMIZAN, ita suke karantawa a wurin ta’alimominsu duk mako, yau wannan Da’irar tana nan daram.
Madalla da ALMIZAN a shekaru 30 muna jinjina da jajirtatun ma’aikatanta da gwarazan dillanta da masu girma na makarantarta. A karshe sai dai na ce babu taken da ya dace da ita kamar yadda na ji an yi mata ranar wannan taro, ALMIZAN IKON ALLAH!
An ciro rubutun nan daga Littafi: ALMIZAN: TARIHI DA GWAGWARMAYARTA
Wannan littafi dai marubuta ne na ALMIZAN kusan goma sha biyu suka bayyana irin gogayyar da suka samu a tsawon wadannan sheekaru na 35, don haka kar ka bari a bar ka a baya wajen mallakar sa.
Za ka iya mallakar littafin cikin sauki ta:
https://selar.com/12j84m
Ko kuma cikin sauki ka yi text ta WhatsApp ta wannan lambar +2348037023343, don ka sayi naka kwafen, a tura ma nantake. N1000 ne kacal.

No comments:
Post a Comment