ALMIZAN DA TALLAR TA A LOKACIN WAKI’O’I
Daga Hasan Baffa
Jaridar ALMIZAN ta kasance daya daga cikin fitattun jaridun Hausa a Nijeriya, musamman wajen isar da sakonnin Harkar Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Tun bayan kafuwar ta a shekarar 1991, ta zama muhimmiyar kafa don yada ilimi da bayanai kan addini, zamantakewa, siyasa, wasanni, sana’a, nishadi, da labarai.
Duk da irin nasarorin da ta samu, jaridar ta sha fuskantar manyan kalubale, musamman daga hukumomin da ke kokarin dakile ayyukanta. ALMIZAN a lokacin waki’o’i da kuma tallar ta ta bambanta da sauran jaridu domin in ana waki’a yin aikin yana kara wuya, haka ma yanayin tallar ta, yayin da kuma masu bukata ke kara yawa domin a nan ne kawai ake samun sahihin labarai da matsaya ta Harkar Musulunci. Domin duk wata sanarwa ko labari da zai fito ta kafar sadarwa na zamani (Socila Media) ba abin amincewa da dogaro ba ne
WAKI’AR ABACHA –12 GA SATUMBA, 1996
A wannan lokaci, jaridar ALMIZAN ta tsinci kanta cikin tsananin matsin lamba. Bayan wani farmaki da jami’an tsaro suka kai gidan Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), an kuma kai samame gidan Shugaban Hukumar Gudanarwar jaridar; Alhaji Hamid Danlami, tare da kama shi, mataimakinsa; Malam Abubakar Abdullahi, da jami’in sashin buga jaridar; Malam Muhammad Shitu Zariya.
An kwace kayan aiki masu yawa, ciki har da kwamfutoci da kwafen jaridar da aka shirya za ta fito a wannan makon. Wannan farmaki ya sa jaridar ta zama tamkar abar tsoro ga hukumomi, inda hakan ya janyo cikas ga bugawa da rarraba jaridar, musamman a garuruwan Katsina, Kaduna, Sakkwato, Funtuwa, da kuma Zariya.
A irin waɗannan garuruwan, an sayar da jaridar ne tamkar kayan fasa kwauri ko kayan maye, inda mai saye da mai sayarwa ne kawai suka san juna. Kasantuwar mafi yawan waki’o’in sun bambanta daga jiha zuwa jiha; wasu gwamnonin sun dauki matsayar fada da Harkar, yayin da wasu suka kau da kai, domin ba za su auka wa jama’arsu ba saboda dalilai na siyasa, biyan bukatun kasashen waje, ko bambancin ra’ayi.
Masu sayarwa da rarraba jaridar sun gamu da matsaloli iri-iri, ciki har da tsarewa, duka, har ma da tilasta wa wasu yin hijira. Duk da haka, masu sayarwa sun nuna jarunta da kwazo wajen ganin jaridar ta isa ga masu karatu. Duk da mawuyacin hali, masu sayen suka nuna tsantsar soyayya da kauna ta hanyar bibiyar hanyoyin da za su samu jaridar ba tare da tsoro ko fargabar abin da zai biyo baya ba.
WAKI’AR DSS – LABARIN MATASAN YOBE
A wani lokaci, Hukumar DSS ta kama wasu ma’aikatan jaridar saboda wani labari da suka wallafa kan kama ko batan wasu matasa 71 a Potiskum na jihar Yobe. A farko, an ɗauka cewa kamun yana nasaba da wannan labari ne. Sai dai daga baya aka fahimci cewa kuskure aka yi wajen kamun. Duk da haka, lamarin ya yi matukar shafar aikin jaridar, musamman wajen samun bayanai cikin sauki.
Sai dai kungiyoyin ’yan jarida ta kasa da na Afrika sun shiga tsakani, har aka samu sakin wadannan ma’aikata ba tare da sun dauki lokaci mai tsawo a tsare ba.
WAKI’AR BUHARI – 12 GA DISAMBA, 2015
Wannan waki’a ita ce mafi tsanani da girma a tarihin Harkar Musulunci. Duk da kasancewar a lokacin an samu ci gaban fasahar sadarwa irin ta Intanet da wayoyin hannu (GSM), matsin tattalin arziki da durkushewar darajar Naira sun yi matukar shafar aikin ALMIZAN, inda hakan ya sa jaridar ta rinka samun matsalolin fitowa akai-akai.
Waki’ar Buhari ta bambanta da ta Abacha sosai. A lokacin Abacha, daidaiku da tarukan Harkar Musulunci ne ake farmaka, yayin a lokacin Buhari, farmakin ya shafi duk wani motsi da halartar tarukan Harkar ne kawai ake aukawa.
Har ila yau, kisan kiyashin Zariya ya rutsa da fiye da mutum dubu, inda suka rasa rayukansu. Duk da gwamnati ta tabbatar da kashe mutum 347 ne, kamar yadda Sakataren Gwamnatin jihar Kaduna, Abbas ya tabbatar a gaban kwamitin bincike da bin diddigin abin da ya faru (JCI).
Wannan kisan kiyashin da gwamnati ta yi, ya rutsa da wakilai da dillalan jaridar da dama. Wannan lamari ya kara jefa ta cikin wani yanayi da har yanzu ba a iya cike gurbin wasu ba.
KALUBALEN AIKI DA KARFIN GWIWA
Duk da kalubalen karancin kayan aiki, tsangwama daga hukumomi, da karancin kudaden da uwa-uba wahalar hada kudaden ciniki a lokacin waki’a, kasantuwar abubuwan da kan-je-ya-dawo na yau da kullum, jaridar ALMIZAN ta taka rawar gani wajen isar da sakonnin Harkar Musulunci. Ta tsaya tsayin daka kan manufofinta, ba tare da karkata ba, duk da irin sukar da ta sha fuskanta daga ciki da wajen Harkar. Ta tsaya kyam a kan manufofi da ka’idoji na aikin jaridar (Editorial Policy).
KAMMALAWA
A yau, jaridar ALMIZAN ta kasance wata sahihiyar kafa ta samun bayanai ga mabiyan Harkar Musulunci da al’umma gaba daya. Duk da matsalolin da ta fuskanta a tsawon shekaru 35, jaridar ta zama alamar jajircewa da gwagwarmaya wajen isar da sako mai ma’ana ga al’umma. Kuma masu tallan ta a shirye suke su bi duk hanyoyi na zamani da kuma fuskatar duk wata waki’a wajen sauke wannan nauyin da ke kansu.
An ciro rubutun nan daga Littafi: ALMIZAN: TARIHI DA GWAGWARMAYARTA
Wannan littafi dai marubuta ne na ALMIZAN kusan goma sha biyu suka bayyana irin gogayyar da suka samu a tsawon wadannan sheekaru na 35, don haka kar ka bari a bar ka a baya wajen mallakar sa.
Za ka iya mallakar littafin cikin sauki ta:
https://selar.com/12j84m
Ko kuma cikin sauki ka yi text ta WhatsApp ta wannan lambar +2348037023343, don ka sayi naka kwafen, a tura ma nantake. N1000 ne kacal.

No comments:
Post a Comment